Zaman dar-dar a birnin Kudus

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jana'izar matashin da aka kashe

'Yan sandan Isra'ila sun yi arangama da Falasdinawa masu zanga-zanga a Gabashin birnin Kudus a lokacin jana'izar matashin nan Bafalasdine da aka kashe a farkon wannan makon.

Dubban masu zaman makoki ne dai suka dauki gawar Mohammad Abu Khdair, lullube da tutar Falasdinawa, suna bi da ita kan titunan birnin.

Dangin marigayin dai sun yi imanin cewa an kashe shi ne, domin yin ramuwar gayya a sakamakon kisan wasu matasa uku 'yan Isra'ila da aka sace a watan jiya.

Wakiliyar BBC ta ce matasan Palasdinawa ne su ka fara jifa da duwatsu a kan 'yan sandan Isra'ila, wadanda suka maida martani ta hanyar harba gurneti mai firgitarwa, amma wadda ba ta haddasa kisa.

Wannan lamarin ya janyo zaman dar-dar a tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.