Malaman Burtaniya sun ja kunne kan Syria da Iraqi

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption 'Yan Burtaniya 500 ne suka shiga fadan da ake yi a Syria da Iraq

Limamai da jagororin addinin Musulunci fiye da 100 a Burtaniya, sun sa hannu kan wata wasika inda suke kira ga musulmai na kasar kada su shiga yakin Syria ko na Iraqi.

Kiran ya biyo bayan kiyasin da hukumomin leken asirin kasar suka yi cewa, kimanin 'yan Burtaniya 500 ne suka shiga fadan da ake yi a Syria da Iraqi.

Wani dan Burtaniya da ya shiga yakin da ake yi a Syria ya shaida wa BBC cewa "Ba zai koma gida ba, har sai ya ga tutar Musulunci tana kadawa a saman fadar sarauniya."

Ya ce ya shafe tsawon shekara daya a Syria yana samun horo na soji da koyon yadda ake hada bama-bamai da kuma harbin abokan gaba.