Al-Baghdadi ya yi huduba a Mosul

Abubakar al_Baghdadi, jagoran ISIS Hakkin mallakar hoto
Image caption A karo na farko Abubakar al-Baghdadi, jagoran ISIS, ya yi huduba a bainar jama'a

Kungiyar 'yan kishin Islama ta ISIS ta fitar da wani faifan video da ta ce na jagoranta ne , Abubakar al-Baghdadi, yana huduba a wani masallaci a arewacin Iraki.

An sa bidiyon ne a intanet, bayan da aka fara rade radin cewa kodai an raunata shi ko an kashe shi. A cikin wannan hoton videon, wanda bisa dukkan alamu aka dauka jiya Juma'a a cikin babban masallacin Juma'a na Mosul, an nuna mutumin da ya kira kansa Khalifa, sanye da wata bakar alkyabba , ga gemu cikakke, yana kira ga daukacin al'ummar Musulmi da su yi masa mubaya'a.

Ya jinjina ma daular Islamar da suka yi shekar kafawa ta ISIS mako guda da ya wuce, a yankin da suke iko da shi a Syria da Iraki.