Kotu a Masar ta yanke daurin rai da rai a kan Badie

Muhammed Badie, shugaban 'yan uwa Musulmi a Masar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Muhammed Badie, shugaban 'yan uwa Musulmi a Masar

Wata kotu a Masar ta yanke hukuncin daurin rai da rai a kan jagoran kungiyar 'Yan Uwa Musulmi, Muhamad Badie da wasu masu ra'ayin kishin Islamar su talatin da shidda.

An yanke musu hukuncin ne kan laifin tunzurawa a tayar da hankali, da kuma kafa shingaye a kan hanya, a lokacin zanga zanga bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin shugaba Muhammad Mursi mai ra'ayin Islama a bara.

Wakiliyar BBC ta ce, tuni da ma wata kotu a Masar din ta yanke hukuncin kisa a kan Muhammad Badien, a wasu shari'o'in biyu, kan rawar da ya taka a zanga zangar.

Kotun a birni Alkahira ta amince da hukuncin kisan da aka yanke kan wasu magoya bayan kungiyar ta 'Yan Uwa musulmi su goma.

Kungiyoyin kare hakkin jama'a dai sun soki lamirin yadda ake yawan yanke hukuncin kisa a kasar ta Masar, suna cewa dalilan siyasa ne ke sa ake hakan.