An "kashe sojoji tara" a Borno

Boko Haram

Rohotanni daga Jihar Borno na cewa wasu 'yan Bindiga sun kai hari a garin Damboa, a yammacin jiya inda suka kashe mutane dadama.

Har yanzu dai ba'a tantance adadin wadanda suka mutu ba a harin.

Sai dai wani dan majalisar dattawan Najeria dake wakiltar yankin, Sanata Ali Ndumeh, ya shaidawa BBC cewe maharan "sun kashe sojoji guda tara, harda babban su."

Dan Majalisar ya kuma ce wadanda suka kai harin sun kuma kashe 'yan sanda biyar da kuma farar hula dadama.

Rohotanni sun kuma ce maharan sun yi kone kone a garin na Damboa.

Ya zuwa yanzu dai rundunar sojin Najeriyar batace komai ba akan harin.

Garin na Damboa wanda ke kudancin Borno, na kusa da garin Chibok, inda a watan Afrilun da ya wuce 'yan Boko Haram suka sace wasu 'yan mata sama da dari biyu.

Har yanzu dai gwamnatin Najeriya na fuskantar matsain lamba akan rashin gano inda 'yan matan suke.

Karin bayani