An kashe sama da mutane 60 a Borno

Boko Haram Hakkin mallakar hoto afp

Rahotanni daga garin Damboa da kuma Konduga a jihar Bornon Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane sama da sittin.

Harin na Konduga an kai shi ne jiya da rana, yayin da kuma aka kai harin na Damboa da yammacin jiya.

Daga cikin wadanda suka mutu a hare-haren harda da sojoji da 'yan sanda da kuma fararen hula dama.

Bayan salwantar rayuka maharan sun kona wurare da dama da suka hada da shaguna da kuma kasuwanni.

Dan majalisar dattawan Najeria dake wakiltar yankin na Damboa, Sanata Ali Ndumeh, ya shaidawa BBC cewe maharan "sun kashe sojoji guda tara, harda babban su."

Sai dai wata sanarwar da rundunar sojin Najeriyar ta fitar dazu tace "sojoji biyar ne suka mutu da wani hafsan soji."

Sanarwar ta kuma ce "'yan ta'adda 50 ne aka kashe a garin na Damboa."

Rohotanni sun kuma ce maharan sun yi kone-kone a garin na Damboa.

Wani mazaunin garin Konduga kuma, ya shaidawa sashen Hausa na BBC cewa harin ya hallaka mutane biyar, kana ya jikkata wasu biyar.

Rohotanni sun ce ana zaman dar-dar a garuruwan biyu.

Garin na Damboa wanda ke kudancin Borno, na kusa da garin Chibok, inda a watan Afrilun da ya wuce 'yan Boko Haram suka sace wasu 'yan mata sama da dari biyu.

Har yanzu dai gwamnatin Najeriya na fuskantar matsain lamba akan rashin gano inda 'yan matan suke.

Karin bayani