'Yan sandan Kenya na bincike a Lamu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A watan jiya ma an kai hari a garin Mpeketoni da ke gabar tekun kasar ta Kenya

'Yan sanda a Kenya sun ce suna gudanar da bincike a kan wasu harbe-harbe a gundumar gabar teku ta Lamu, inda aka bayar da rahoton cewa an kai hari a kan wani caji ofis.

An kuma ce an kona gidaje da dama a harin.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta Kenya ta ce harbe-harben sun lafa.

Zuwa yanzu dai ba tabbatar ko an jikkata wani a harin ba, ballantana wanda ya kai harin; amma a bana mayakan kungiyar Al-Shabaab sun kara kaimi wajen kai hare-hare a yankin, ciki har da wanda aka kai a watan jiya a kan garin Mpeketoni, inda aka kashe mutane fiye da sittin.

Karin bayani