Sabuwar dokar intanet a Rasha

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A baya Shugaba Vladimir Putin ya sanya hannu a kan wata dokar da ta karawa hukuma iko da intanet

Majalisar wakilai ta Rasha ta amince da wani kudurin doka wanda zai bukaci shafukan intanet na sada zumunta da wasunsu na kasashen waje su rika ajiyar bayanan 'yan kasar a cikin gida.

Daftarin dokar dai ya wajabta wa shafukan sada zumunta na intanet na kasashen wajen ne su rika adana bayanai a kan al'ummar Rasha a cikin kasar.

Hakan na nufi ke nan wajibi ne kamfanonin inanet na kashen waje su kakkafa na'urorin kwamfiyuta na adana bayanai, wato servers, a kasar ta Rasha, in kuma suka ki a toshe su.

Wadanda suka rubuta kudurin dokar sun ce ana matukar bukatar ta ne don kare kasar ta Rasha da al'ummarta, amma masu suka sun ce hakikanin manufarta ita ce baiwa gwamnati karin iko da intanet din da kuma damar kaiwa ga bayanan al'ummar kasar da ke shiga shafukan na intanet.

Kudurin dai na bukatar amincewar majalisar dattawa da sa hanun shugaban kasa kafin ya zama doka.

Karin bayani