An kirkiro kyamara mai tashi sama

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Airdog, kamar yadda sunansa ke nunawa, tamkar kare ne da ke bin mutum amma a sama

Wadansu sababbin fasahohi biyu na fatan kawo sauyi a yadda masu sha'awar wasanni ke daukar kansu a hoton bidiyo.

Fasahohin na kananan jiragen sama marasa matuka, wato Hexo+ da Airdog, suna tashi ne su yi ta bin mai amfani da su daga sama ta hanyar bibiyar wayar salula komai-da-ruwanka (a bangaren Hexo+) ko kuma na'urar da ake daurawa kamar agogon hannu (a bangaren Airdog ke nan).

Ko wanne jirgi mara matuki na dauke da kyamara, da na'urar da ke daidaita shi a sama, sannan kuma zai iya tafiyar minti 10 zuwa 15 a sama da batiri guda; zai kuma iya gudun mil kusan 40 a duk sa'a daya.

Jiragen biyu dai sun zarta abin da aka nema na jarin da ake bukata don kera su a shafin inatnet na Kickstarter, inda jama'a ke karo-karo don zuba jari a wata sabuwar fasaha.

Wani dan kasar Latvia ne mai suna Edgars Rozentals ya kirkiri Airdog, ya kuma shaid wa BBC cewa ko da yake tunanin kera jirgin sama mara matuki don ya rika bin mai shi duk inda ya yi ba sabon abu ba ne, wannan ne karo na farko da za a sayar da shi kamar sauran kayayyakin da mutum ka iya shiga kasuwa ya saya.

Ya kuma yi bayani a kan dalilin kirkirar wannan jirgi mara matuki: "Akasarin abokan aikina suna yin wasannin motsa jiki masu hadari; sai wasu daga cikinsu suka ce me zai hana mu yi wata na'ura da za ta rika daukarmu hoton bidiyo idan muna sulu a kankara, misali?"

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption A hannu, kamar agogon hannu, ake daura na'urar da ke Airdog ke sansana yana bi

Mista Rozentals ya kuma ce jirgin da kansa yake komai, amma duk da haka "za ka iya sarrafa shi ka sauya nisan tahinsa a sama ko ma ka kashe shi ya daina binka".

Ya kuma ce don tabbatar da kiyaye faruwar hadari, suna nan suna kokarin sanya wa jirgin wata na'ura wacce za ta iya gane wuraren da bai kamata ya shiga ko ya bi ba.