Chibok: An yi zanga-zanga a Abuja

Masu zanga zanga akan matan Chibok Hakkin mallakar hoto AFP

Daruruwan Jama'a ne suka yi zanga-zanga dazu a Abuja, don mastsawa gwamnati lamba akan nemo 'yan matan Chibok da 'yan Boko Haram suka sace.

Mutanen, sun hada da masu kare hakkin jama'a da 'yan kungiyoyi masu zaman kansu.

Sun yi maci har zuwa fadar shugaban kasar amma jami'an tsaro basu barsu sun shiga ciki ba.

Daya daga cikin wadanda suka jagoranci macin ya shaidawa sashen Hausa na BBC cewa, "dole ne gwamnati tayi wani abu akan sace 'yan matan."

Tun a watan Afrilu ne dai 'yan Boko Haram suka sace 'yan mata sama da dari biyu daga makarantar sakandiren mata dake garin Chibok a jihar Borno dake arewacin kasar.

Daga bisani shugaban kungiyar, Abubakar Shekau ya fidda wani hoton bidiyo inda yace zai saida 'yan matan a kasuwar bayi.

Lamarin yasa jama'a a ciki da wajen Najeriya matsawa gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan lamba akan ta gaggauta kubutar da su.

A kwanakin baya, iyayen matan sunce idan gwamnati bata dawo masu da su ba, to zasu kai maganar gaban Majalisar Dinkin Duniya.

Ita dai gwamnatin Najeriyar ta ce tana kokarin kubutar da 'yan matan amma ba lalle ne ta bayyana hanyoyin da take bi ba.