An kashe mutane 13 a Kenya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mutane fiye da sittin ne suka rasa rayukansu a harin da aka kai Mpeketoni a watan jiya

Akalla mutane 13 ne aka bayar da rahoton sun rasa rayukansu a wadansu hare-hare guda biyu da aka kai a kan wasu al'ummun Kenya dake kusa da gabar teku.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta Kenya ta ce mutane tara aka akshe a harin da aka kai yankin Gamba dake karamar hukumar Kogin Tana, yayin da wasu hudu kuma suka rasa rayukansu a karamar hukumar Lamu da ke kusa da iyakar kasar da Somaliya.

An kai harin na biyu ne dai a kan wani ofishin 'yan sanda a garin Hindi wanda ke karamar hukumar ta Lamu; Hindi na kusa da Mpeketoni, inda aka kashe fiye da sittin a wani harin da aka kai a watan jiya.

Cibiyar ba da agajin gaggawa ta gwamnatin Kenya ta rubuta a shafinta na Twitter cewa 'yan sanda suna daukar matakan da suka dace a wuraren da aka kai harin.

Har yanzu dai ba a san wanda ke da alhakin aki hare-haren ba, amma kungiyar mayakan sa-kai ta Somaliya, wato Al-Shabaab ta kaddamar da hare-hare da dama a yankin.

Kungiyar Red Cross ta ce ta aike da ma'aikatan ba da agajin gaggawa yankin.

Wani wakilin BBC a Nairobi ya ce an kona gidaje da dama a Hindi. Ya kuma ce tun bayan harin watan jiya 'yan sanda suka kara karfafa matakan tsaro a yankin.

Shugaba Uhuru Kenyatta dai ya zargi 'yan bangar siyasa da kai harin na watan jiya, duk kuwa da cewa kungiyar Al-Shabaab ta dauki alhakin lamarin.

Karin bayani