An sako limami da 'yan arewa 11 a Abia

Image caption Ana zargin sojojin Nigeria da muzgunawa fararen hula

Sojojin Najeriya sun sallamo limamin masallacin Jumu'ar nan da wasu 'yan arewa 11 wadanda suka kama a cikin wani samame kan wani masallaci da wasu kasuwanni a jihar Abia da daren ranar Lahadi.

An sako Liman Bashir Idris da na'ibinsa da sauran mutane 10 da aka kama yayin samamen a garuruwan Aba da Lokpanta

Sai dai Rahotanni sun ce har yanzu akwai sauran mutane biyu da ake tsare da su.

Kawo yanzu rundunar tsaron Nigeria ba ta ce komai ba game da batun.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da al'ummar arewacin Nigeria ke ci gaba da zargin cewar jami'an tsaro na gallaza musu a yankin kudancin kasar.

A cikin watan Yuni ma, sojoji sun tsare Hausawa 'yan arewacin Nigeria su kusan 500 a jihar Abia kuma bayan shafe makonni a daure, sannan suka sake su.

Karin bayani