Boko Haram: Mata 60 sun kubuta

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Amurka na neman Abubakar Shekau ruwa a jallo

Jami'an tsaro a Nigeria sun ce, wasu mata da 'yan mata su sama da sittin sun tsira daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram.

Wadanda suka tsira din na daga cikin mata fiye da 68 da ake zargin 'yan Boko Haram sun sace a watan da ya wuce, a kusa da garin Damboa da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Nigeria.

Gwamnatin kasar ta kaddamar da bincike kan yadda matan suka bace.

Wasu rahotanni sun ce wata kila matan sun kubuta ne ranar Juma'a, lokacin da wadanda suke tsare da su, suka tafi kai hari kan wani sansanin soji.

A daren Juma'ar dai sojojin Nigeria suka ce sun kashe sama da mayakan Boko Haram 50 a dauki ba dadin da suka yi da su a kusa da Damboa.

Har yanzu dai 'yan kungiyar ta Boko Haran suna rike da 'yan matan 'yan makaranta sama da 200 da suka sace a Chibok a watan Afrilu.

Kungiyar Boko Haram ta yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane a Nigeria tun daga shekara ta 2009.

Hakkin mallakar hoto NEMA
Image caption Rikici Boko Haram ya raba dubban mutane da muhallansu