An samar da na'urar hana daukar ciki da ake iya sarrafawa daga nesa

Image caption Na'urar za ta bukaci chanji bayan kowadanne shekaru 16.

An samar da wata naura mai kunshe da sanadarin hana daukar ciki da ake iya sarrafawa da wata na'ura daga nesa a jihar Massachusetts ta Amurka.

Ana saka naurar mai karamcin gaske ne ciki jikin mace, inda za ta rika fitar da sanadarin Levonorgestrel.

Takan yi hakan ne a kowace rana har tsawon shekaru 16, amma kuma ana iya dakatar da ita ta hanyar amfani da wani maganadisun sarrafa na'urori daga nesa.

Aikin samar da na'urar dai ya samu goyon bayan Bill Gates kuma za a kai ta domin likitoci su yi gwajinta a shekara mai zuwa, mai yiwuwa a fara sai da ta a shekarar 2018.

Yadda take aiki

Image caption Na'urar za ta taimaka wa mutanen da ke mance wa da su sha magani.

An saka wasu 'yan kananan rumbunan adana sanadari a jikin na'urar mai fadin sentimita daya da rabi.

Akwai wani karfin lantarki da kadan da ke narkar da marufin rumbun sanadarin, abin da zai sa ya fitar da sanadarin mai yawan microgram 30 zuwa cikin jiki.

''Samun damar kunna ta, da kashe ta ya samar da wata sakewa ga wadanda ke kayyade iyali,'' Inji Dokta Robert Farra.

Kalubale

Sai dai Kalubale na gaba ga masu kera na'urar shi ne tabbatar da cikkakken tsaro ga na'urar domin hana wani ya kunna ko kasheta ba tare da sanin matar aka saka wa ita ba.

Ana iya amfani da fasahar wajen saka wasu magungunan a jiki bayan na hana daukar ciki.

Sai dai Simon Karger, shugaban sashen aikin tiyata a Jami'ar Cambridge, ya ce irin wannan na'urar da ake sakawa cikin jiki na fuskantar kalubale mai yawa da kasada.

Karin bayani