Zargin bullar cutar Ebola a Ghana

Image caption Cutar Ebola na saurin kisa

Ma'aikatar lafiya a kasar Ghana ta ce ma'aikatan lafiya na duba wani majinyaci da ake zargin ya kamu da mummunar cutar Ebola mai saurin kisa.

Sanarwar Ma'aikatar lafiyar ta ce an samu rahoton kamuwa da cutar ne a karamin asibitin Nyaho da ke Accra babban birnin kasar.

Ta ce an kebe marasa lafiya da ma'aikatan asibitin kuma an ba su tufafin kariya.

Cutar Ebola ya zuwa yanzu ta kashe mutane sama da 460 tun bayan bullar ta a kasar Guinea cikin watan Fabrairu, inda ta yadu zuwa makwabtan kasashe irinsu Liberia da Saliyo.

Ebola ita ce cuta mafi saurin hallaka mutane a duniya ya zuwa yanzu, kuma ba ta da riga-kafi ko magani.

Ma'aikatar lafiyar ta ce ta dauki matakan kariya don haka mutane su kwantar da hankalinsu.