Sisi ya yi nadamar hukunta 'yan Aljazeera

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kalaman Al-Sisi na jawo martani

Wani rahoto ya ambato Shugaban kasar Masar Abdul Fattah al-Sisi ya ce ya yi fatan ace 'yan jaridu ukun nan na gidan Talabijin din Aljazeera da aka daure a kurkuku a watan da ya gabata, da ba a gurfanar da su gaban shari'a ba.

Peter Greste, da Mohamed Fahmy da kuma Baher Mohammed an ya ke musu hukuncin zaman gidan yari daga shekaru bakwai zuwa goma bayan da aka same su da laifin taimakawa Kungiyar 'yan ta'adda.

Jaridar al-Masry al Youm a karshen mako ta ambato Mr Sisi na cewa shari'ar na da "mummunar sakamako."

Kalaman na sa dai ya jawo martani daga iyalan 'yan jaridun.

Gwamnatocin kasashen ketare da kafafen yada labarai da Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun zargi Hukumomin Masar da takaita 'yancin fadar albarkacin baki.

Gidan Talabijin na Aljareeza kuwa ya ce hukuncin ya sabawa hankali da tunani da ma duk wani kamanceceniya da adalci.

Karin bayani