An nemi a biya 'yan arewa mazauna Enugu diyya

Image caption Katin shaidar 'yan arewa mazauna Enugu ya janyo kace nace

A Najeriya, kungiyar kare hakkin bil' Adaman nan ta Civil Liberties Organsation, ta shigar da kara a babbar kotun tarayya da ke Enugu, tare da hadin gwiwar wani jigo na 'yan arewa mazauna jihar.

An shigar da karar ce bisa zargin da ake yiwa gwamnatin jihar Enugu na tilasta wa 'yan arewa mazauna jihar yin wani katin shaida.

Karar dai, wadda aka fara saurare a ranar Litinin, tana nema a soke katin shaidar, sannan kuma a mayar wa 'yan arewa kudin katin Naira dubu dai-dai da aka karba daga hannunsu

Harwa yau karar na neman a biya su kudi Naira Miliyan dubu hamsin a matsayin diyyar keta masu hakki.

Wannan katin shaidar dai ya janyo cece kuce a Kasar.