An kwance tulin bama-bamai a Gombe

Hakkin mallakar hoto
Image caption Jahar Gombe na fama da matsalolin tsaro

Hukumomin tsaro a jihar Gombe sun kwance bama-bamai masu yawa a cikin wata motar da aka ajiye a wata makarantar sakandare.

Dazu da rana ne dai jami'an tsaron suka killace yankin Tashar Dukku, inda makarantar ta jeka-ka-dawo take, kana suka kwashe bama-baman da kuma motar dake dauke da su.

Rundunar 'yan sandan jihar Gomben ta bayyana cewa, a cikin bama-baman 12 har da wasu guda 3 dogaye na sundukai, da wasu gajeru, yayin da wasu guda 5 kuma aka sanya su cikin akwatunan makamai na soji, wadanda da sun tashi, to kuwa da sun yi gagarumin ta'adi.

Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin dasa bama-baman.

Wannan ne karon farko da aka samu irin wannan lamari na bama-bamai a makaranta a jihar ta Gombe.

Sai dai a watannin baya rahotanni sun ce hukumomin jihar sun gaggauta rufe makarantu gab da bayar da hutun karshen zangon karatu, sakamakon wasiku daga masu tayar da kayar baya wadanda ke barazanar kai hare-hare a makarantun a Gomben.

Jahar Gomben dai ta yi fama da hare-haren bam da suka janyo hasarar rayuka da dama.