Isra'ila ta hallaka Falasdinawa tara

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Isra'ila ta ce ta kai hare-haren nen don mayar da martani

Falasdinawa tara ne suka rasa rayukansu a hare-haren da Isra'ila ta kai da jiragen saman yaki a zirin Gaza.

Kungiyar Hamas ta ce an kashe mayakanta shida a wani hari da aka kai kusa da Rafa.

Jami'an ba da agajin gaggawa a zirin na Gaza dai sun tabbatar da mutuwar mutane biyu ne a harin, amma an yi amanna cewa baraguzan ginin da aka kaiwa harin sun binne wasu mutanen hudu. An kuma kashe mutum na bakwai a wani harin na daban.

Kafin nan kuma an kashe wadansu mayakan sa-kai Falasdinawa a wani harin wanda aka kai a kusa da wani sansanin 'yan gudun hijira da ke tsakiyar zirin na Gaza.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hare-haren ne don mai da martani ga hare-haren da ake kaiwa kudancin Isra'ila da rokoki. Sun kuma ce sun kai hare-haren ne a wuraren da ake aikata ta'addanci da maboya makaman roka.

Sai dai kuma kungiyar Hamas ta ce Isra'ila za ta dandana kudarta saboda kashe mata mutane da ta yi.

Karin bayani