An bude taro kan fansho na Duniya a Abuja

Image caption Ana sama da fadi da kudaden fansho a Najeriya

An fara wani taro irinsa na farko a kan harkokin fansho a nahiyar Afrika, inda masu ruwa da tsaki a fannin za su yi musayar ra'ayoyi game da ci gaban da aka samu da kuma kalubalen da bangaren ke fuskanta.

Taron na kwanaki biyu da ake yi a Abuja, babban birnin Najeriya, ya zo ne a lokacin da masu karbar fansho da dama a kasar ke shan wuya kafin su karbi kudaden fanshonsu.

Haka kuma rahotanni sun nuna cewa ana samun masu karbar fanshon da ke rasa rayukansu a lokacin da suke kan layi domin karbar kudaden da ba su taka kara sun karya ba.

Shekaru goma ke nan da aka yi wa tsarin fansho a Najeriya garambawul, sai dai har yanzu wasu na ganin da sauran rina a kaba.

Sai dai kuma ranar Talatar da ta gabata ne Shugaba Goodluck Jonathan ya rattaba hannu a kan wata sabuwar dokar, wacce ake fatan za ta kawo sauyi sosai a harkar ta fansho.