Mummunar yunwa a Sudan ta Kudu

Image caption Yadda Iyalai suka fada cikin yunwa a Sudan ta kudu

Kasar Sudan ta Kudu ta sake afkawa cikin rikici a watan Disamba amma wannan karon ba da abokiyar gabarta ba Jamhuriyar Sudan.

Rikicin tsakanin jagorori ne wadanda suke da bambancin kabila.

Rikicin ya jawo tabarbarewar ayyukan noma sannan kuma ya dai-dai ta kiwon dabbobi abinda ke nufin yunwa na mamaye al'umma.

Don ganin yadda Sudan ta Kudu ta zama saboda yakin da ta afka na watanni shida; ba sai ka kai ta da nisa ba ko filin saukar jiragen sama da ke a babban birnin Juba ya ishe ka.

Akwai tankunan yaki da kuma bindigogin harbo jiragen sama a karshen titin jirgin filin saukar jiragen saman.

Image caption Sojojin Sudan ta kudu na artabu da 'yan Tawaye

Abinda ya rura wutar rikicin wanda yake ci gaba da daidaita kasar shi ne zargin yin juyin mulki da tsohon mataimakin Shugaban Kasar Riek Machar ya yi ga tsohon abokin gabarsa Shugaba Salva Kiir.

Rikicin siyasar da hanzari ya rikide ya koma na kabilanci kuma ya yadu.

Rikicin dai an sami rahotannin kisan kare dangi da fyade, da kuma amfani da kananan yara a matsayin soji.

Sama da mutane miliyan daya ne yakin ya daidaita, sannan kuma an kashe akalla mutane dubu goma.

Abinda yake dada nuni da irin halin da mutane suka shiga shine yadda za ka ga gidajen da aka kona, gidajen da galibi aka yi su da yunbu inda galibi mutane ke zaune an rusa su, dabbobi an tarwatsa su an kuma kwashe abincin da aka ajiye a rumbu.

Image caption Wata mata da danta sun gujewa rikicin Sudan ta kudu

Wakilin BBC ya hadu da wata Nyachane Nien-wata siririyar mata mai shekaru 17 tana zaune a kan wata katifa a wani Asibiti na Leer wanda aka kona wani bangarensa.

Yayinda rikicin ya isa ga garinsu ta gudu inda ta shafe makoni tana boye a wajen wani kurmi inda akwai ruwa tana rike da danta dan watanni tara.

Idan dare ya yi kuma sai ta koma dandabariyar kasa ta kwana; haka suke rayuwa.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasashen cewa mutane 50,000 za su iya mutuwa nan da wasu 'yan watanni saboda yunwa a Sudan ta kudu.

Mutanen da suka mutu a yakin basasar na watanni shida bai taka kara ya karya ba idan aka kwatanta da wadanda za su mutu saboda karancin abinci da cututtuka.