Ingila: Za a sa Intanet mai sauri a jiragen kasa

Image caption Sanya intanet mai sauri a jiragen kasan na daga tsarin inganta sufurin

Za a kashe makudan kudaden tara wajen sanya intanet mai sauri a jiragen kasa na fasinja a fadin Ingila da Wales.

Intanet din da za a sa a jiragen, nan da shekaru uku zuwa hudu da mutane za su rika amfani da ita za ta linka ta yanzu sau goma wurin sauri.

Gwamnati ce za ta samar da wani kashi na kudin aikin fam miliyan 90 daga kudaden tara da aka ci kamfanin safarar jiragen kasa na Network Rail.

Ofishin kula da harkokin kamfanin ne ya ci tararsa saboda jinkirin jiragen zuwa wasu muhimman wurare na dogon zango a cikin shekaru biyar.

Masu lura d al'amura suna ganin aibun cin tarar kamfanin jiragen kasan kan rashin gudanar da aiki yadda ya kamata, domin hakan na hana kamfanin samun kudaden da zai inganta ayyukansa.

Intanet din da za sa za ta kasance tana tare da jiragen a duk inda suke maimakon tsarin yanzu inda wasu wuraren ba a samunta.

Haka kuma za a fara la'akari da hanyoyin da ake samun fasinjoji masu yawa wajen sanya intanet din da farko kafin ya zama na gaba daya.

An ci tarar kamfanin ne saboda jinkiri a hanyoyin dogon zango da suka hada da Cross Country da East Coast da First Hull da First TransPennine Express da Grand Central da Virgin da First Great Western da East Midlands Trains da kuma Greater Anglia.