Shugaba Abbas ya bukaci Isra'ila ta yi taka tsan-tsan

Jagoran Palasdinawa Mahmud Abbas Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jagoran Palasdinawa Mahmud Abbas

Jagoran Palasdinawa Mahmoud Abbas ya yi kira ga Isra'ila da kada ta zafafa game da hare-haren sojin da ta ke kaiwa Zirin Gaza.

Ya kuma ce akwai bukatar kara jefa yankin cikin wani mawuyacin hali.

Jawabin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ta ce ta na da damar yin amfani da dakarunta ta kasa domin dakatar da cigaba da harba makaman rokar da ake yi daga zirin na Gaza.

Rahotanni sun ce da tsakar dare ne kuma aka gargadi wasu iyalai su yi kaura daga yankin na Zirin Gaza.

Wani magidanci ya ce tun da misalin karfe uku da rabi ne sojoji suka kira su ta wayar tarho, suka bukaci su su bar gidajensu, kuma kimanin mintuna goma bayan sun fice aka kai ma gidajen farmaki.