Zargin tafka magudi a zaben Afghanistan

Magoya bayan Abdullah Abdullah Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban magoya bayan Abdullah Abdullah sun taru a tsakiyar birnin Kabul

Dan takarar shugaban kasa a Afghanistan Abdullah Abdullah ya yi watsi da sakamakon zaben da aka sanar yana zargin cewa a tafka magudi.

Mr Abdullah ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga dubban magoya bayansa wadanda suka taru a tsakiyar birnin Kabul, inda ya yi ikirarin cewa shi ya kamata a ba nasara a zaben da a aka gudanar.

Dan takarar shugaban kasar ya kuma yi Allahwadai da zaben inda ya jaddada cewa shi da magoya bayansa ba za su taba amincewa da wannan sakamakon ba.

A bangare guda kuma Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce duk wani mataki da aka dauka na karbe mulki ba bisa ka'ida ba a kasar ka iya janyowa Amurka ta dakatar da tallafin da take baiwa Afghanistan.