Guguwa ta afkawa kudancin Japan

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Amurka ta umarci jiragen yakinta da su bar sansanin soji na birnin Okinawa.

Mahaukaciyar guguwa mafi muni da ba'a taba ganin irinta ba cikin shekaru goma wadda ta fada tsibiran kudancin Japan a yanzu ta isa gabashin kogin China kuma karfin ya fara raguwa yayin da take kadawa yankin kan tudu.

Guguwar wadda aka yi wa lakabi da Neoguri hade ruwan sama ta na tafiyar fiye da kilomita dari biyu a cikin sa'a guda yayin da ta ratsa tsibirin Okinawa inda aka umarci mutane kimanin dubu dari biyar su nemi mafaka ko kuma su kauracewa yankin.

Ga alama matakan rigakafin da aka sanar sun yi tasiri kasancewar ba a sami mutane da dama da suka ji rauni ba.

Sai dai duk da haka guguwar na da karfi kuma tana iya yin lahani.

Karin bayani