Za a nuna Fim kan yakin Biafra

Chimamanda Ngozi Adichie
Image caption An shirya fim ne daga littafin marubuciyar nan 'yar Nijeriya, Chimamanda Ngozi Adichie

Za a fara nuna wani fim mai cike da takaddama da aka shirya kan yakin basasar Nijeriya a shekarun 1960.

Za a fara nuna fim din ne a gidajen silima daga watan Agustan wannan shekarar bayan hukumar tace fina-finai ta ba da izinin yin haka.

An tsara kaddamar da fim din mai suna 'Half of a Yellow Sun' a kan yakin Biafra a watan Afrilu, amma hukumar tace fina-finan kasar ta ce ba za a amince da wasu bangarorinsa ba.

An shirya fim din ne daga littafin marubuciyar nan 'yar Nijeriya, Chimamanda Ngozi Adichie.

Kimanin mutane fiye da miliyan daya ne suka mutu a yakin basasar, wanda ya faro sakamakon yunkurin ballewa na lardin kudu maso gabashin Nijeriya.

Sai dai wasu na fargabar cewa fim din ka iya janyo rikicin kabilanci a kasar.