'Mun san inda 'yan matan Chibok suke'

Air Marshal Alex Badeh Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Manyan hafsoshin tsaron Najeriyar sun ce kubutar da `yan matan na bukatar taka-tsan-tsan.

Hukumomin tsaro a Najeriya sun sake jaddada cewa sun san inda ake tsare da 'yan matan sakandaren Chibok su fiye da 200 da 'yan Kungiyar Boko Haram suka sace.

Manyan hafsoshin tsaron Najeriyar sun shaida wa majalisar koli da ke kula da harkokin mulkin kasar cewa kubutar da 'yan matan na bukatar taka-tsan-tsan.

Jami'an tsaron sun kuma yiwa majalisar bayani kan irin kalubalen da kasar ke fuskanta ta fuskar tsaro.

Wannan dai ba shi ne karon farko da jami'an tsaro ke ikirarin cewa sun san inda ake boye da 'yan matan makarantar sakandaren Chibok ba.

A kwanakin baya babban hafsan tsaron Najeriyar, Air Marshal Alex Badeh ya ce jami'an tsaro sun san inda 'yan makarantar suke, sai dai ya jaddada cewa akwai bukatar a yi kaffa-kaffa wajen ceto su don gudun kada su hallaka.