'Ba za a sake sace dalibai a Nigeria ba'

Shugaba Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Jonathan ya koka kan karuwar dalibai da ke barin makarantu a kasar

Shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan ya ce gwamnatin kasar ba za ta sake bari a sace dalibai da ke karatu a makarantun kasar ba.

Da ya ke jawabi a lokacin da ya ke kaddamar da kwamitin tabbatar da tsaro a Makarantu, Shugaba Jonathan ya ce karuwar yaran da ke barin makaranta ba tare da sun kammala ba, abu ne da ba za a amince da shi ba.

Shugaban kasar ya ba da misali da jihar Borno inda ya ce yanzu haka yara da dama ba sa son zuwa makaranta, saboda barazanar ayyukan 'yan ta'adda. Lamarin da ya ce ya yi muni matuka har ma a wasu yankunan kashi 30 cikin 100 na yara ne kadai ke zuwa makaranta.

An bullo da shirin tabbatar da tsaro a makarantun kasar ne don tabbatar da kare rayukan dalibai da malamai da kuma dawo da kwarin gwiwar iyaye wajen barin 'ya'yansu su ci gaba da halartar makaranta.