Bore: Za a hukunta wasu sojojin Nigeria

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Kotun sojin na sauraron wasu kararrakin da ake zargin sojoji da aikatawa a wasu wurare

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da gurfanar da wasu sojojinta gaban kotun soji na musamman da ake zargin su da yin bore a Maiduguri a watan Mayu.

Kakakin rundunar Manjo Janar Chris Olukolade ya tabbatarwa da BBC hakan, sai dai bai bayyana yawan sojojin da aka gurfanar din ba.

Haka kuma kotun sojin na sauraron sauran kararrakin da ake zargin sojoji da aikatawa a wasu wurare.

A watan Mayun da ya gabata ne wasu sojojin kasar da suka fusata suka harbi motar shugabansu da ke Maiduguri, Manjo janar Ahmadu Mohammed bayan da 'yan kungiyar Boko Haram suka kashe wasu sojoji a wani kwanton bauna da suka yi musu.

Wannan al'amari dai ya fusata sojojin, wadanda suka dora alhakin hakan akan babban kwamandan na su, ko da yake a wancan lokacin rundunar ta musanta boren tana mai cewa harbin sama sojojin suka yi.