An dakatar da bada lasisin bindiga a Nigeria

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ana kai hare hare da bindigogi a Nigeria

Rundunar tsaro ta 'yan sandan Najeriya tace ta haramta anfani da kananan makamai a tsakanin al'ummar Kasar.

Rundunar ta bayyana dakatar da bayar da lasisin mallakar sabbin bindigogi a kasar, har sai bayan babban zabe na shekara ta 2015.

Umarnin na rundunar tsaro ta 'yan sandan dai , wani kandagarki ne dan kaucewa anfani da bindigogi ta hanyoyin da ba su dace ba.

Kwararru dai sun ce dokar ba zata tsananta tsaro a kasar ba.

'Abinda ya kamata ace shine a budawa 'yan kasar domin baiwa kansu kariya' in ji wasu kwararrun kan harkokin da suka shafi tsaro.