Za a halalta tabar wiwi a Amurka

Ganyen wiwi
Image caption Jihohi 23 na Amurka sun ba da damar sayar da tabar wiwi ga masu sha don magani

A ranar Talata ne za a halalta sayar da tabar wiwi ga masu sha don nishadi a cikin jihar Washington ta Amurka.

Da wannan mataki, Washington ita ce jiha ta biyu da ta amince da sayar da wiwi ga masu sha don nishadi bayan Colorado, wadda a yanzu ke samun miliyoyin daloli na haraji daga cinikin tabar wiwin.

Sai dai hukumomi a jihar Washington za su tsaurara sharudda a kan wannan sabon mataki na tu'ammali da tabar wiwin.

Ya zuwa yanzu an ba kantuna 25 lasisin sayar da tabar, ko da yake hukumomi sun yi imani cewa adadin zai karu a nan gaba.

Jihohi 23 kenan a Amurka suka ba da damar saye ko sayar da tabar wiwi ga masu sha don magani.