Taron ECOWAS zai tattauna cutar Ebola

Image caption Cutar Ebola na neman mamaye kasashen yankin bayan matsalar Tsaro.

A yau Alhamis , za a bude taron koli na kungiyar raya tattalin arzikin Kasashen Afrika ta Yamma wato ECOWAS a kasar Ghana.

Taron na kwana biyu, ana sa ran zai maida hankali ne kan batun annobar zazzabin nan mai kisa wato Ebola, wanda rahotanni suka ce cutar na neman mamaye kasashen yankin.

Kawo yanzu dai annobar na cigaba da yaduwa a kasashen Saliyo da Liberia da kuma Guinea

Rahotanni sun ce zazzabin Ebola ya hallaka kimanin mutane 467.

Har ila yau kuma, taron zai yi nazari kan matsalolin tsaro a wasu Kasashen Kungiyar.