Ana ci gaba da kashe mutane a Gaza

Image caption Isra'ila na amfani da manyan makamai da jiragen yaki

Akalla mutane 20 ne aka kashe a dare mafi muni a hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Zirin Gaza a yankin Palasdinu, kamar yadda jami'ai suka bayyana.

Ma'aikatar lafiya ta ce mafi yawansu sun mutu ne a harin da aka kai wani gida da kuma wurin sayar da abinci a unguwar Khan Younis, abinda ya sa adadin wadanda suka mutu ya kai 76.

'Yan bindiga a Gaza sun ci gaba da harba makaman roka zuwa Isra'ila, sai dai babu wata illa da suka yi kawo yanzu.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi gargadin cewa lamarin ka iya kazancewa fiye da yadda ake tsammani.

Mutane 17 ne ciki harda kananan yara biyar da mata uku aka kashe a harin na Khan Younis.

Isra'ila bata ce komai game da kisan farar hular na baya-bayan nan ba.

Karin bayani