Gaza:Mutane 25 sun mutu a harin Isra'ila

Image caption Falasdinawa ma sun harba rokoki zuwa wasu biranen Isra'ila.

Wasu hare-hare da Isra'ila ta kai ta sama cikin dare sun yi sanadin mutuwar mutane fiye da ashirin da biyar a zirin Gaza a wani abu da ke zaman somawar wani babban farmaki.

Isra'ila ta ce ta kai hari kan wurare sama ga 100 a zirin na Gaza yawanci kan sansanonin harba makaman roka.

Jami'an Falasdinawa sun ce daga cikin wadanda aka kashen akwai wani jami'in kungiyar 'yan gwagwarmaya ta Islamic Jihad, wanda ya mutu sa'adda aka jefa bam kan gidansa a garin Bait Hanoun.

''Mun karbi mutane da dama da suka samu raunukka a asibiti. Shida daga cikinsu sun mutu- uku mata, uku maza. Akwai kuma wasu yara uku 'yan kasa ga shekaru hudu ko biyar sun samu raunukka.'' Inji wani likita a asibitin garin na Bait Hanoun, Ayman Hamdan.

Sai dai Firayin Ministan Isra'ila Benyamin Natanyahu, ya ce Falasdinawa ne ke amfani da fararen hulla a zaman garkuwa.

Karin bayani