'Da ya kashe mahaifinsa kan tabar wiwi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dokokin Najeriya dai sun haramta shan tabar wiwi.

'Yansanda a Nijeriya sun kama wani saurayi bisa zargin kashe mahaifinsa ta hanyar sara masa gatari a jihar Enugu da ke kudu maso gabascin kasar.

Ikenna Onu, dan kimanin 20, ya kai ma mahaifin nasa Christopher Onu hari ne bayan jan-kunnen da uban ya yi masa na ya daina zukar tabar wiwi.

''Wannan shawara ta harzuka Ikenna abin da ya sa ya dauki gatari ya kwantara wa uban ga kai; ya yi masa rotse wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa daga bisani.'' Inji Kakakin 'yansandan na jihar Enugu DSP Ebere Amarizu.

Wannan lamarin wanda ya faru a garin Agu-Abose na jihar ta Enugu, na zuwa ne yayin da wasu kungiyoyi ke kokarin bayar da shawarar janye haramcin shan wasu kananan miyagun kwayoyi da suka hada har da tabar ta wiwi a kasashen yankin Afirka ta yamma.

Karin bayani