Sudan: Shekaru 25 na mulkin Al Bashir

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Al Bashir tsohon Soja ne

A lokacin da Omar al-Bashir ya kwace mulki a wani juyin mulkin da ba a zubar da jini ba a watan Yunin 1989, bai yi fice ba a matsayinsa na jami'in soja- amma a yanzu an san shi a duk fadin duniya.

Ya jagoranci Sudan na tsawon lokaci fiye da kowa a tarihin kasar, kuma duk da cewar yana fuskantar tuhuma a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya watau ICC, amma kuma yana da farin jini a tsakanin al'ummar kasar sa.

Dan siyasa kuma mai fafutukar bin tafarkin Musulunci, Hassan al-Turabi ne ya citsa juyin mulkin sojin a shekarar 1989.

A lokacin Mr Turabi ya na cikin gwamnatin, Sudan tana bin tsarin tsatsaurar ra'ayin Musulunci.

Masu kaifin kishin Islama irinsu Osama Bin Laden duk sun koma Sudan, sannan an kafa dokar shari'ar Musulunci da kuma kyamatar wadanda ba Musulmi ba a Kudancin Sudan.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ya nada farin jini a tsakanin al'ummar Sudan

Kafin juyin mulkin soji a kasar, gwamnatin Sudan da kungiyar 'yan tawaye ta Sudan People's Liberation Movement (SPLM) na gab da sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya.

Sai dai daga bisani sai Mr Bashir da mukarrabansa suka zabi hanyar ci gaba da yaki babu kakkautawa.

'Nasara'

A shekarar 1999, Shugaba Bashir ya samu nasara a kokawar mulki tsakaninsa da Mr Turabi.

Tun daga wannan lokacin gwamnatin ta a jiye shirinta na sake fasalin kasar da kuma makwabtanta.

Kuma babban burin kasar ya koma ci gaba da kasance kasa daya dunkulalliya.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An dade ana yakin basasa a Sudan

Kasar Sudan na da arzikin man fetur amma kuma miliyoyin 'yan kasar na fama da talauci.

Sannan babu zaman lafiya a kasar musamman a kudanci.

An yi ta fama da rikici a Darfur da ke a yammacin kasar sannan kuma kudancin kasar ya samu 'yancin kai a shekara ta 2011.

Shin waye Al-Bashir ?

  • An haife shi a ranar 1 ga watan Junairun 1944
  • Ya na da mata biyu Fatima Khalid da Widad Babiker
  • Ya shiga aikin soja a 1960
  • Ya samu horo tare da rundunar sojin Masar sannan ya yi yaki tare da dakarun Masar lokacin yaki da Isra'ila a shekarar 1973
  • Ya yi juyin mulkin soja a shekarar 1989
  • Ya sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Kudu da Arewa a shekara ta 2005
  • Kotun ICC ta zarge shi da aika ta laifukan yaki a Darfur
  • Ya lashe zaben shugaban kasar Sudan a shekara ta 2010
  • Ya tabbatar da samun 'yancin kan Sudan ta Kudu a shekara ta 2011
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Al Bashir da amaryarsa Widad Babiker