Hulda da bankuna ta wayar salula ta kai ta Fam Biliyan 1 a rana

Hakkin mallakar hoto PA Wire
Image caption Hakama hada-hadar kudin ta wayar salula na samun karbuwa a kasashen masu-tasowa.

Sakamakon wani nazari ya nuna cewa hada-hadar kudade da ake yi da bankuna ta wayar salula da shafukan intanet ta kai ta Fam biliyan daya a rana a Burtaniya.

Binciken wanda kungiyar ma'akatan bankuna ta Burtaniya da ta EY suka gudanar dai ya nuna cewa ana amfani da fasahar wajen huldar da ta kai ta fam biliyan 6.4 a mako.

Sai dai ba su nuna yawan hada-hadar da ake yi ta wayar salula kawai ba, amma sun ce yawanta ya karu kwarai da gaske.

Binciken ya kuma gano cewa akalla akan sauko da manhajar hulda da banki 15,000 a wayoyi kowace shekara.

Image caption Wasu a kasashen masu tasowa na dari-dari da wannan salon saboda kasadar cin karo da 'yan damfara.

A jimlace an sauko da manhajojin hulda da bankuna ta wayar salula miliyan 14.7- abin da ke nuna sauko da su ya karu da miliyan 2.3 daga watan janairu zuwa yau.

Sai dai rahoton binciken ya gano cewa har yanzu mutane da yawa sun fi son su yi amfani da na'urar komfuta da aka girke wajen hada-hada da manyan kudade; bisa ga shiga ta wayar salula.

''A yayin da masu hulda da bankuna ke son saukin da ke ga bincika yawan kudin da ya rage musu a asusu ta wayar salula, sun fi amfani da babbar komfuta wajen aika kudi masu yawa ko neman bashin gida,'' inji rahoton.

Karbuwar da amfani da wayar salula ko na'urar komfuta wajen hulda da bankuna a kasar ta samu, ta haifar da raguwar shiga zauren banki kwarai da gaske.

Sai dai duk da haka yana da muhimmanci kwarai har yanzu wajen karbar bashin gida ko na kudi.

Karin bayani