'Yan Ghana na neman mafakar siyasa a Brazil

Image caption Wasu 'Yan Ghana sun soma neman gindin zama a Brazil

Masu goyan bayan 'yan kwallon kafar Ghana kusan 200 ne suke neman mafakar siyasa a Brazil bayan da suka shiga a matsayin 'yan yawan bude ido domin kallon gasar cin kofin duniya.

Wani babban jami'in 'yan sanda a Brazil din a birnin Caxias do Sul yace 'yan kasar Ghanan dai sun ce su musulmi ne da suka tserewa rikicin addini a kasar su ta haihuwa.

Amma ya ce da dama daga cikinsu a yanzu sun bingire da neman ayyuka a cikin kasar ta Brazil.

'Yan sandan sun ce da zarar an kammala gasar cin kofin duniyar a ranar Lahadi, suna saran wasu 'yan Ghanan su 1,000 zasu sake zuwa domin neman mafakar siyasa.

Tuni dai akai waje da Ghanan a gasar cin kofin duniyar.