Gaza: An kashe mutane 9 a wani sabon hari

Image caption Sai dai Falasdinawa sun harba rokoki sama ga 100 zuwa cikin Isra'ila a cikin sa'oi 24.

Rahotanni daga kudancin Gaza na cewa hare haren da Isra'ila take kaiwa ta sama sun yi sanadiyyar kashe mutane 9 da ke kallon gasar cin kofin duniya a wani wajen shan kofi da ke bakin ruwa a garin Khanyounis.

A yanzu dai mutane fiye da 60 ne ake jin cewar sun mutu sakamakon hare haren da Isra'ilan ta fara kaiwa ta sama a kan zirin Gaza a wannan makon.

Babu dai rahotannin wadanda suka jikkata, amma kungiyar Hamas na ci gaba da harba rokoki cikin Israila.

Babban Sakataren Majalisar Dunkin Duniya Ban Ki-Moon, ya yi gargadin cewa halin da ake ciki a Gaza ka iya rikidewa zuwa wani gagarumin Yaki

Karin bayani