LG ya kera agogon da ke sanar da iyaye inda yaransu suke

Image caption Kizon dai yana iya aiki ko da ruwa ko datti ya taba shi.

Kamfanin LG ya sanar da kera wani agogon hannu da ke ba iyaye damar sanin inda dansu yake da kuma sauraren abin da yake yi.

Na'urar mai suna Kizon na amfani da GPS da kuma karfin sadarwar intanet na wi-fi wajen sanin inda wanda ke daure da agogon ya ke; kuma yakan aika ne da sakon ga wata manhaja ta Android.

LG yayi agogon ne domin iyayen da yaransu ba su fara makaranta ba ko wadanda ke firamare.

Sai dai wasu sun nuna shakku ga fito da wannan fasaha.

''Ka da iyayen su dogara kacokan kan wannan na'urar kawai. Domin wannan zai ba da tsaron da ba na gaskiya ba ne kawai,'' inji Peter Bradley, jami'i a wata kungiyar ba da agaji ga yara mai suna Kidscape.

Ya kara da cewa ''duk da wannan yara na bukatar a sanar da su abubuwan da ke da hadari a gare su- musamman hadarin da ke ga bakuwar fuska.''

Image caption Agogon dai yana abin latsawa daya ne tak.

Shi ma mukaddashin daraktan kamfanin Emma Carr, ya ce dole ne iyaye su san cewa duk wata fasahar nuna inda mutum ya ke tana tattare da nata matsaloli na tsaro, musamman idan mai amfani da ita yaro ne.

''Kamfunnan da ke kera wadannan na'urorin dole ne su bayyana abin da suke yi na kare bayanan da na'urar ke daukowa domin tabbatar da iyayen yaro ne kawai za su iya ganin bayanai game da inda yake,'' inji shi.

Wata mai magana da yawun kamfanin na LG bata ce komai ba game da wadannan batutuwan da aka tayar ba.

Kamfanin na koriya ta kudu dai ba shi be ya fara tallata wannan na'urar ba- domin wasu kananan kamfunnan irin su KMS Solutions, Tinitell da Filip duk sun yi tallar irin wannan na'urar- kodayake LG shi ne mashahurin kamfani na farko da ya tallata na'urar.

Karin bayani