Taron kasa ya kasa daidaitawa kan rabon arziki

Image caption Wani lokaci a cikin wannan watan ne za a kammala taron.

A Najeriya, mahalarta babban taron kasar sun kasa samun jituwa a yunkurin da suke yi, na daidaitawa kan rabon arzikin kasa ta hanyar maslaha.

Zauren taron dai ya kaure da hayaniya a lokacin da kwamitin tabbatar da yin kome cikin maslaha ya gabatar da rahotonsa.

Kwamitin ya bada shawarar a yi wa jihohin yankin Niger-Delta mai arzikin mai karin kashi 5% akan abinda suke samu daga kudaden shiga da ake samu daga danyen mai, tare da kebe wa jihohin shiyyar arewa-maso-gabas kashi 5% don raya yankin.

To amma sai Wakilai daga shiyyar kudu maso yamma da takwarorinsu na shiyyar kudu-maso-gabas, suka yi watsi da wannan bukatar suna cewa ba za su tashi a tutar babu ba.

Karin bayani