Ma'aikata na yajin aiki a Birtaniya

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ana saran ma'aikata miliyan daya za su fito zanga-zangar

Kungiyar kwadago a Birtaniya ta bayyana cewa, yajin aikin da ma'aikatan gwamnati ke yi shi ne mafi girma da aka taba yi tun shekarar 2011 a sakamakon takaddama da ake yi kan batun albashi da wasu batutuwan.

Kungiyoyin da ke wakiltar malaman makaranta da ma'aikatan kashe gobara da ma'aikatan gwamnati da na kananan hukumomi su ne suka shirya yajin aikin.

Su waye ke yajin aikin?

Yawancin su ma'aikatan kananan hukumomi ne da ke goyon bayan malaman makarantu daga kungiyar Unison da GMB. Mambobin kungiyar malaman makaranta NUT da na kashe gobara FBU da ta NIPSA da kuma ta PCS suma sun bi sahun su.

Dalilin yajin aikin:

Matsalar da ke damun kungiyoyin ita ce ta biyan kudaden albashi.

Mafi yawan ma'aikatun gwamnati albashinsu ya daskare tun 2010 ga kuma tashin farashin kaya da ya karu da kashi 1 cikin 100 a 2014-15.