An hana dalibai yin azumi a China

  • 11 Yuli 2014
Image copyright AFP
Image caption Akwai musulmai da dama 'yan kabilar Uighur a Kashgar

Dalibai da dama na Jami'a a yankin Xinjiang na yammacin China, sun shaidawa BBC cewa an hana su yin azumin watan Ramadan.

Daliban ba sa son a bayyana sunansu, saboda tsoron abubuwan da ka iya biyo baya, idan suka yi magana kan wani batu mai janyo kace nace.

Hana yin azumin na zuwa ne yayinda ake samun karuwar tashin hankali a yankin.

Wasu daga cikin dalibai musulmai sun shaidawa BBC cewar an tilasta musu cin abinci tare da malamansu domin a tabbatar ba sa yin azumi.

Wadanda suka ki cin abinci za su iya fuskantar hukunci mai tsanani daga wurin hukumomin jami'ar.

Kamar yadda wasu dalibai su uku suka bayyana, dokar haramtawa musulmai yin azumi na aiki a duka jami'o'in da ke lardin.

'Matakin Gwamnati'

Ba wannan bane karon farko da China ta ke hana mutane yin azumin watan Ramada a lardin Xinjiang.

Amma matakin na wannan karon na zuwa ne a lokacin da ke zaman dar-dar.

China na zargin masu tsatsaurar ra'ayin Musulunci da kaddamar da hare-hare a 'yan kwanakin nan.

A ranar Alhamis, wata Kotu a Xinjiang ta yanke wa mutane fiye da 30 hukuncin dauri a gidan yari saboda sauke bidiyon 'yan ta'adda ta hanyar intanet.

'Yan kabilar Uighur sun ce gwamnati ce ke janyo rikicin saboda gallaza musu ta fuskar addinni da kuma al'ada.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun zargin China da fakewa da batun barazanar ta'addaci ta hanyar daukar matakai masu tsauri a kansu.