Ghana ta karyata masu neman mafaka a Brazil

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu neman mafakar sun je kallon kwallo ne

Gwamnatin Ghana ta bayyana cewar mutane kusan 200 da ke neman mafakar siyasa a kasar Brazil sun sharara karya ne kawai.

Magoya bayan Ghana din da suka je Brazil kallon kwallo, sun nemi mafakar siyasa, inda suka ce su Musulmai ne sun gujewa rikicin addinni a kasar su.

Mataimakin ministan yada labarai na Ghana, Felix Kwake Ofosu ya ce "Hujjar da suka bayar don neman mafaka, karya ce kawai domin babu rikicin addinni a Ghana."

Sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar, ta ce babu rikicin addinni a Ghana, kuma kasar na daga cikin mafi zaman lafiya a nahiyar Afrika.

Shugaban 'yan sanda a birnin Caxias da Silva Mel inda 'yan Ghanan ke neman mafaka, ya ce watakila mutanen da neman aikin yi ne saboda lardin na daga cikin inda ke bunkasa a kasar ta Brazil.

Karin bayani