Hanya daya ta goge bayanai a waya

Hakkin mallakar hoto EBAY
Image caption 'Hanya daya ta hana dawo da bayanai da hotunan da ke cikin waya shi ne lalata wayar gaba daya'

Wasu kwararru sun yi gargadin cewa hanya daya da za a iya kawar da bayanai ko hotunan da ke cikin waya sai dai a lalata wayar gaba daya.

Wani kamfanin harkokin tsaro na kasar Czech ne ya yi nasarar samo wasu dubban hotuna da aka dauka da waya wadanda kuma aka goge su.

Kamfanin mai suna Avast, ya yi amfani da wasu kayayyaki da kowa zai iya saya a kasuwa, ya samo hotunan daga wasu tsofaffin wayoyin salula da aka saya.

Sauran abubuwan da aka samu a wayoyin sun hada da wasikun email da rubutattun sakonni da shafukan da aka nemo ta Google.

Duk da cewa, wayoyin salula suna da tsarin goge duk wasu abubuwa da aka sanya a wayar, ya mayar da ita kamar yadda kamfani ya yi ta tun farko (factory setting), Avast ya gano wasu tsofaffin wayoyin, ba sa goge ainahin abubuwan da aka dauka ko sanyawa a kan wayar.

Hakkin mallakar hoto

Kamfanin na Avast, ya ce hotuna 40,000, da ya samo daga tsofaffin wayoyi 20 da aka saya, sama da 750 na mata ne da suke tsirara.

Wasu 250 kuma hotunan tsirara ne na mazan da suka mallaki wayoyin tun da farko.

Bayan wadannan da sauran abubuwa, har da sunaye 250 da adireshin email da yawa.

Kamfanin ya gargadi masu wayoyin salula manya na komai-da-ruwanka da su tabbatar sun rika maye hotuna da sauran abubuwan da suka sa a wayar (overwrite) kafin su rabu da su, ba kawai goge su (deleting) ba.

Sai dai kuma kamfanin Google ya ce kamfanin Avast, ya yi amfani da tsofaffin wayoyi ne na komai-da-ruwanka, ba na zamani ba.