'Doka kan binciken salula a Birtaniya'

Image caption Sai dai Mr Cameron ya ce bayanan da za a bincika ba su hada da maganar ko sakon da aka aike ba.

Majalisar dokokin Burtaniya na kokarin gaggauta kafa wata doka da za ta ba jami'an tsaro iznin neman bayanai daga wayoyi da shafukan intanet na jama'a.

Farayin Minista David Cameron ya ce ya samu goyon bayan dukkanin manyan jam'iyyun uku wajen wannan aikin na gaggawa da ba saban ba.

Ya ce ana bukatar daukar mataki da gaggawa domin kare jama'a daga miyagu da 'yan ta'adda, bayan da Kotun Tarayyar Turai ta soke ikon da suke da shi a da.

Sai dai masu fafutukar kare hakkin dan adam na gargadin cewa hakan zai ba damar lekon asirin mutane.

Amma Mr. Cameron ya kare matakin wajen wani taron manema labarai tare da mataimakinsa Nick Clegg yana mai cewa wannan dokar ba za ta kawo wani abu sabo ba.

Amma kawai za ta hada ne da kamfunna masu mazauni a kasashen waje da ake amfani da wayoyi da sadarwar intanet nasu a Burtaniya.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Majalisar na son kafa dokar ne cikin mako daya kawai.

Za a nada wani babban jami'in diplomasiyya da zai yi aiki tare da sauran kasashe wajen hanzarta aika ko karbo bayanan da aka nema daga kamfunnan.

Mr. Cameron ya kuma ce ya cimma wata yarjejeniya da jagorar jam'iyyar Leba Ed Miliband ta kara fadada ikon saka ido da jami'an tsaro ke bukata .

''Muna fuskantar barazana ta hakika ga tsaronmu daga kungiyoyi masu aikata miyagu laifukka, daga aiyukka masu lalata da kananan yara, daga rikicin Syria, da bullar ISIS a Iraki da kuma Al-shabab a gabascin Afrika.'' Inji Mr. Cameron.

Ya ci gaba ya cewa'' ni ba zan zama farayin ministan da zai fito ya yi wa jama'a jawabi bayan wani harin 'yan ta'adda ba yan cewa akwai wasu matakan da da ya dauke su da harin bai faru ba.''

Karin bayani