Amurka ta yi tayin sasanta rikicin Gaza

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Daga cikin wadanda aka kashen har da mutane takwas 'yan gida daya.

Shugaba Barack Obama na Amurka ya yi tayin taimakon Amurka wajen samun tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas a daidai lokacin da Isra'ila ke kara matsa kai hare-hare kan zirin Gaza.

A cikin wata hira ta wayar tarho da Farayin ministan Isra'ila Benyamin Natanyahu, Mr. Obama ya jaddada bukatar bangarorin biyu su kaucewa abin da zai kai ga karuwar tashin hankalin.

Rahotannin baya-bayan nan na cewa mutane fiye da 90 ne aka kashe a hare-haren da Isra'ilar take kaiwa ta sama a kan Gaza, a matsayin martani ga rokokin da Falasdinawa ke harbawa kan manyan biranenta.

A watan Nuwamban shekara ta 2012 lokacin da aka yi fada na karshe tsakanin Isra'ila da Hamas, Amurka ta samu taimakon Masar wajen cimma tsagaita wuta, sai dai a wannan karon Masar din ba ta nuna aniyar shiga tsakanin ba.

Karin bayani