'Yan sanda sun dakile hari a Abuja

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rundunar 'yan sandan ta bukaci a sa idanu sosai a tashoshin mota

Rundunar 'yan sanda a Najeriya ta ce ta dakile wani hari da 'yan ta'ada suka kitsa kai wa a wasu wuraren shiga motoci inda jama'a ke taruwa a Abuja.

'Yan sandan sun ce sun gano shirin kai hare-haren ne bayan wasu rahotanni da suka samu na sirri.

A wata sanarwa da kakakin rundunar Frank Mba ya fitar ya bukaci masu kula da tashoshin mota su sa idanu sosai kan duk wasu kayayyaki da za a shiga da su tashohin.

Mr Mba ya bukaci 'yan kasar da su sake lura sosai game da yanayin tsaronsu, kana su kai rahoton duk wani abu da ba su amince da shi ba.

Karin bayani