An samu koma baya a yaki da AIDS

Hakkin mallakar hoto ThinkStock
Image caption Lamarin ya nuna wahalar da ke tattare da samun maganin cutar ta kanjamau

An sake gano kwayar cutar AIDS ko SIDA a jikin wata yarinya da aka haifa da kwayar cutar da ake ganin an yi mata magani tana karama.

An yi wa yarinyar yar shekara hudu daga Mississipi, ta Amurka, maganin cutar ne tun lokacin tana jaririya, kuma har watan Maris da ya wuce babu alamun cutar ba tare an yi mata magani ba tsawon shekara biyu.

To amma kuma wasu gwaje-gwajen da aka yi mata a makon da ya wuce sun nuna alamun kwayoyin cutar a jikinta.

Sakamakon binciken ya haifar da koma baya na fatan cewa, maganin cutar a farko farkon lokaci na iya kawar da ita gaba daya.

A da dai ana da kyakkyawan fatan cewa yarinyar za ta yi rayuwa ba tare da kwayar cutar ba.

Wata yarinyar kuma da ake gwajin maganin cutar a kanta wadda aka ci gaba da ba ta magani ba tsayawa ba ta nuna alamun dawowar kwayoyin cutar ba.

Hakkin mallakar hoto SPL

Magungunan rage radadin cutar ta kanjamau na iya yakar kwayoyinta a cikin jini, to amma bincike ya nuna za su iya buya a cikin kwakwalwa.

Daga zarar an dakatar da yi mata magani sai kwayoyuin su sake fitowa daga inda suka buya.

Kawo yanzu mutum daya ake ganin an yi wa maganin cutar ta kanjamau.

A 2007, aka sake wa Timothy Ray Brown zubin bargon kashi daga wani tsatso wanda baya kamuwa da kwayar cutar.

Yanzu sama da shekaru biyar da yi masa wannan aiki har yanzu bai nuna alamun cutar ba.