Ana cinikin fatar damisa a China

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana tsare da dubban damisoshi a China, inda aka ba da damar sayar da fatunsu

Mahalarta wani taron duniya a kan kiyaye dabbobi sun ce a karo na farko China ta amince a bainar jama'a cewa ta bayar da dama a yi cinikin fatun damisa.

A cewar mahalartan da jami'an taron, a baya hukumomin China ba su taba bayar da rahoton faruwar hakan ba a wurin Taron Duniya kan Yaki da Cinikayyar Dabbobi da Tsirran da ke Fuskantar Barazanar Karewa.

Sai dai kuma yayin ganawar kwamitin dindindin na taron, wadda ke wakana a Geneva, an bayar da rahoton cewa China ta ce ta haramta cinikin kasusuwan damisa.

Wani mai halartar taron ya ce: "Wani wakilin China ya ce, 'ba mu haramta cinikin fatun damisa ba, amma mun haramta cinikin kasusuwanta'".

Hukumomin taron na kare halittu masu fuskantar barazana sun tabbatar da cewa wakilin na China ya fadi haka.

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen China, Qin Gang, ya shaida wa Sashen Sinanci na BBC cewa ba zai iya tannatar da amincewar kasar tasa ba, amma a cewarsa China za ta bincika ta kuma yaki cinikin fatun damisa.

An yi amanna cewa ana tsare da damisa tsakanin 5,000 da 6,000 a China, kuma kungiyoyin kare halittu sun sha bayyana bukatar kawo karshen cinikayyar fatun namun daji.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Damisa na cikin dabbobin da suka fi fuskantar hadarin karewa

Masana dai sun yi amanna cewa "kiwon damisa" a China ya haifar da karuwar farauta da safarar dabbobin a wadansu wurare.

Sun kuma ce amincewar da China ta yi za ta sa a kara matsa mata lamba ta kawo karshen harkar.

Rahotanni sun ce gonakin da ake tsare da dabbobin suna samar da damisa mai rai da ma sassan jikinta don haramtacciyar cinikayya a fadin duniya.

Karin bayani